YADDA MAMACI ZAI GANE SHI MATACCE NE

 YADDA MAMACI ZAI GANE SHI MATACCE NE,


mamaci ba zai gane shi matacce ba ne a karon farko, saboda abun zai masa kamar a mafarki, zai ga yana kuka yana shure shure yana kaiwa da komowa har ya kai ga anamishi wanka, a kuma ɗaukeshi zuwa magabarta duk zai na ganin abun kamar a mafarki,


Bai yadda cewa ya zama  gawa ba,

sai bayan an bun ne shi yanaji ana cewa kutura ƙasa ta ɓangaren can, ganan baiji ƙasa ba, ku kawo ɗanyan kasa ta bangarennan, a wannan lokacin zai ringa cewa mutane mai kuke kokarin yi ne,


Bayan kowa ya bar maƙabarta, anbarshi shi ka dai a cikin kasa, sai Allah yasa a dawo masa da ransa ya ɓude idon sa ya farka a cikin matattu,


Daga lokacin zai fara murna ya farka daga mummunan mafarki,


A Wannan lokacin sai ya godewa Allah 

ya yi yun ƙurin miƙewa sai yaji ansuturtashi, an daddamkeshi da wata riga marar hannu, babu aljihu ba wuya, sai ya fara mamaki da tambaya a karon farko,


A ina nake haka? Ina ne nan? ba wutar lantarki, ba AC, ba fanka, an rufeni ta kowani ɓangare,


Mai na ke yi a nan ?


To a nan ne zai gane lallai yana cikin kasa,zai kuma tabbatar cewa lallai yanzu ba mafarki bane mutuwace ta gaskiya,


A wannan lokacin zai yi wani sauti mai karan gaske, yana kiran yan uwansa kamar yadda ya ke yi anan duniya 

idan yana bukatar dauki


Zairinka  kiran sunayen ƴan uwansa,

Amma zai ji babu mai amsa masa, to daga nan zai soma fahimtar cewa allah ne ka ɗai zai agaza masa, to a lokacin zai din ga fadan astagfirullah,


Allah natuba ka agaza mini kaji kaina,


Ya na furta haka a cikin tsoro mai tsanani,


Idan mutumin kirki ne a lokacin mala'iku biyu zasu bayyana a gareshi cikin kyakkyawan fuska, sai su tallafeshi suce kwantarda hankalinka daga nan zai fara  samun kyakkyawan agaji,


Jama'a mu tuba zuwa ga Allah, mu gyara ayyukan mu, musani cewa babu makawa sai mun riski mutuwa, ya Allah ka sa mu cika da imani amin.


Dan Allah Ku tura xuwa GRP 5 SBD Al ummar Annabi su amfana

Comments

Popular posts from this blog

CHRISTIANS ARE ALWAYS CONSPIRING TO OVERTHROW THE SUPREME GOD OF THE UNIVERSE FROM THE THRONE AND INSTALL JESUS CHRIST

🤣lol

THE MANY LIES CHRISTIANITY WAS MADE WITH.