YESU ALMASIHU BAI ZO DAGA SAMA BA HAIHUWARSA AKAYI ANAN DUNIYA . KUMA KAFIN A HAIFE SHI BABU SHI SAM

 YESU ALMASIHU BAI ZO DAGA SAMA BA HAIHUWARSA AKAYI ANAN DUNIYA . KUMA KAFIN A HAIFE SHI BABU SHI SAM :


Ina mamakin yadda kiristoci da sauran Pastors suke watsa karya acikin mutane wai Yesu daga sama yazo duniya .


 Idan haka ne dukkan Annabawan Allah tun daga Annabi Adam har zuwa Annabi Muhammad (SAW) suma dukkansu daga sama suka zo duniya domin Allahn da ya aiko Yesu Almasihu suma shi ya aiko su .  


Amma abin mamaki su kiristoci sun kebe Yesu shi kadai suka ce wai shi kadai ne yazo daga sama domin wai dama shi a sama yake kafin yazo duniya . 


Idan muka karanta Baibul acikin Matthew 1 aya 18-26 da Luke 1 aya 26-31 da kuma Suratul Maryam aya 16- 36 zamu ga tarihin yadda Maryam ta haifi Yesu Almasihu ta hanyar bishara da mala'ika yayi ma Maryam cewa zata haifi yaro . 


Mala'ika Jib'rilu bai cema Maryam ba Yesu zai sauko daga Sama ya shiga cikin ta domin ta haife shi . Amma yace zaki haifi yaro kuma sunansa Yesu .  

Bayan an haifi Yesu sai Baibul ya fada mana acikin Luke 2 aya 21 cewa any ma Yesu Kaciya a tsuliyarsa alhali yana da kwana takwas a duniya . 


Yanzu zaku iya cewa Allahn naku ne akawa kaciya a tsuliyarsa alhali yana da kwana takwas da haihuwa ? 


Zaku iya cewa Maryama ta haifi Allahn ku har yasha nonon ta ? 


Zaku iya cewa Allahnku ne yake girma har ya kai shekaru 33 a duniya ? 


Haba kiristoci , ya kamata kuyi tunani mana ! 


Yanzu tambayar da zanyi muku shine , idan har kunce Yesu yana sama tun kafin a haife shi , to minene sunansa a can saman kafin a haifeshi ? 


Baibul ya gaya mana cewa bayan Maryam ta haifi Yesu sai aka sanya masa suna Yesu kamar yadda yazo a cikin Luke 2 v 21 . 


Magana ta biyu itace idan kunce Yesu yana Sama , Baibul yace Annabi Iliya da Annabi Idris dukkansu sun tafi sama da ransu kuma basu mutu ba kamar yadda yazo acikin Genesis 5 v 24 da Hebrews 11 v 5 da kuma 2Kings 2 v 9-12 . 


Mala'iku ma ai a sama suke rayuwarsu . Sukan sauko kuma su koma sama . Amma Yeso bai sauko daga sama ba , an haife shine anan duniya . 


Annabi Yahaya dan Zakariya shima bisharar haihuwarsa tazo ne daga sama ta hanyar mala'ika in ji Baibul acikin Luke 1 v 13 -16 , haka shima Annabi Isma'ila shima bisharar haihuwarsa tazo ne daga sama ta hanyar Mala'ika kamar yadda baibul ya fada acikin Genesis 16 v 9-12. Ashe ba Yesu ne kadai ba akayi bisharar haihuwarsa acikin Baibul . .

Comments

Popular posts from this blog

CHRISTIANS ARE ALWAYS CONSPIRING TO OVERTHROW THE SUPREME GOD OF THE UNIVERSE FROM THE THRONE AND INSTALL JESUS CHRIST

Crazy Talks

ARE CHRISTIANS SAVED BY GRACE?