YESUN DA KIRISTOCI KE KIRA ALLAH YANA DA KANNE MAZA DA MATA DA MAHAIFIYARSA TA HAIFA INJI BIBLE.

YESUN DA KIRISTOCI KE KIRA ALLAH YANA DA KANNE MAZA DA MATA DA MAHAIFIYARSA TA HAIFA INJI BIBLE.

 MATTHEW 13 AYA 55-57 , DA MARK 6 AYA 3

A kullum idan ina son inyi dariya har cikina yayi ciwo sai in tuna yadda kiristoci ke Kiran Yesu Almasihu Allahnsu alhali shi wannan mutum dan Adam mai suna Yesu Almasihu yana da mahaifiya da ta haife shi mai suna Marryam kamar yadda Alkur'ani da Bible suka bamu labari . Ita wannan baiwar Allah mai daraja da tsoron Allah itace ta yi renon Yesu Almasihu , ta yi masa wanka, ta bashi abinci da abinsha , ta yi masa duk abubuwan da mahaifiya kewa jaririnda ta haifa . Ashe kaga Yesu Almasihu yana da Uwa ,sai dai baya da Uban da ya haife shi acikin mutane kamar yadda Adam bai da Uba ko Uwa , ita ma Hawwa'u bata da Uwa, Mala'iku basu da uwaye . 


Sai in tambayi kaina cewa Kiristoci suna bautar wani mutum da suka ce shi Allah ne , amma wai Allahn nan nasu yana da Uwa , kuma shi yana ci kuma yana sha ,har ma yana fitsari kuma yana kashi ,yana rashin lafiya kuma harma sun ce wasu kattin mutane sun kashe Allahn nan nasu mai suna Yesu . 


Wannan wane irin Allah ne mai kama da mutane har ma yana da bukata irin ta dan Adam ?


 Sai abin ya bani tausayi ga kiristoci masu irin wannan addinin bautar mutum mai kashi da fitsari da wasu bukatu kuma ya bani dariya . Sai in kara godiya ga Allah da yayi mu musulmi . 


A yau kuma nayo wani dan bincike mai ban dariya acikin Bible. Binciken da niyyo shine ,bayan Maryam Uwar Yesu da kiristoci ke kira cewa shine Allahnsu , ta haife shi , akwai wani mutum mai suna Yusuf wanda ake cema Joseph the Carpenter.  


Shi kafinta ne , sai aka daura masa aure da Mahaifiyar Yesu , sai ta haifi yara shida ko fiye da haka maza da mata . 


Wadannan yaran baibul ya kira su yan'uwan Yesu Almasihu domin Uwarsu daya . Don haka su dukkan su Kannen Yesu ne . Idan kuna son ku ga wannan labari da baibul ya fada muna sai ku karanta Matthew 13 aya 55-57 da kuma Mark 6 aya Uku .


 Bible din har sunayen kannen Yesu ya fada . Sa annan shi kansa Yesu din Bible ya kira shi Son of Joseph the Carpenter acikin wadannan ayoyin domin shi Joseph ko Yusuf Shi ne ya auri Mahaifiyar Yesu da kiristoci ke kira Allahnsu . 


Abin ban dariya shine yaya wani mutum zai auri mahaifiyar da ta haifi Allah mai suna Yesu idan har da gaske ne Yesu Allah ne ? Yaya za ace Allah yana da kanne mazansu da matansu ? Yaya za a ce wainAllah Allah yana da Uwa , har ma ace ma wani mutum mai suna Joseph wai shine Ubansa ? 


Ina kira ga Kiristoci wallahi ku gudu kubar wannan addini mai bautar mutane a matsayin Allah domin ku tsira .

Comments

Popular posts from this blog

CHRISTIANS ARE ALWAYS CONSPIRING TO OVERTHROW THE SUPREME GOD OF THE UNIVERSE FROM THE THRONE AND INSTALL JESUS CHRIST

Crazy Talks

PAUL vs JESUS – CONTRADICTIONS IN THE BIBLE